Sudan: 'Yan Adawa Za Su Gudanar Da Zama A Birnin Paris
(last modified Tue, 12 Mar 2019 14:59:06 GMT )
Mar 12, 2019 14:59 UTC
  • Sudan: 'Yan Adawa Za Su Gudanar Da Zama A Birnin Paris

Kungiyoyi da jam'iyyun adawa a kasar Sudan za su gudanar da wani zama a birnin Paris na kasar Faransa, domin tattauna hanyoyin kawo karshen matsalolin da kasar ta samu kanta a ciki.

Shafin yada labarai na Arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyi da jam'iyyun siyasa a kasar Sudan suna shirin gudanar da wani zaman tattaunawa  a birnin Paris na kasar Faransa, inda wata kungiyar farar hula dag akasar Amurka za ta jagoranci zaman.

Babbar manufar zaman tattaunawar dai ita ce duba matsalolin da kasar Sudan ta ke fama da su ta fuskokin siyasa da tattalin arziki da zamantakewa, da kuam lalubo hanyoyin kawo karshen danbarwar da kasar ta fada a ciki a wannan lokaci.

Daga cikin kungiyoyi da jam'iyyun siyasa da za su halarci taron har da babbar jam'iyyar adawa ta Sadiqul mahdi, da kuma wasu kungiyoyi daga yankin darfur, da ma wasu jam'iyyun siyasa na kasar.

Za a fara gudanar da taron ne dai aranar 20 ga wanann wata na Maris da muke ciki.