Harin Ta'addanci Ya Ci Rayukan Mutum 13 A Mozambique
(last modified Mon, 18 Mar 2019 05:06:37 GMT )
Mar 18, 2019 05:06 UTC
  • Harin Ta'addanci Ya Ci Rayukan Mutum 13 A Mozambique

Wasu 'Yan bindiga sun hallaka fararen hula 13 a arewacin kasar Mozambique

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyen Ulo mai gumshe da gidaje sama da dari dake tsakanin lardunan Nabajo da Maculo.

Hukumomin kasar ta Mozambique sun tabbatar da kai harin, inda suka ce 'yan ta'addar sun yi amfani da makamai kamar wuka da adda a kan fararen hula, sannan sun kone gidajen mutane a anguwar Nangan, lamarin da ya yi sanadiyar salwantar fararen hula 13 daga cikinsu akwai mata da kananen yara.

Jami'an 'yan sandar kasar Mozambique sun fitar da rahoton cewa daga cikin maharan akwai 'yan kasashen Tanzaniya da Somaliya.

Tuni dai gwamnatin kasar Mozambique din ta dora alhakin harin kan kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alqa'ida.