Najeriya: Ana Ci Gaba Da Takun Saka Tsakanin APC da INEC
(last modified Tue, 19 Mar 2019 06:19:00 GMT )
Mar 19, 2019 06:19 UTC
  • Najeriya: Ana Ci Gaba Da Takun Saka Tsakanin APC da INEC

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta soki hukumar zaben kasar akan zabukan da za a sake yi a wasu jahohin kasar.

Jam’iyyar ta APC ta kuma zargi hukumar zaben mai zama kanta da hada baki da jam’iyyar adawa ta PDP.

Jan’iyyar ta APC ta bayyana matsayinta ne akan zaben kwanaki kadan da su ka rage kafin sake yin zabukan a jahohin kano, Plateau, Adamawa, Rivers, Benue da Bauchi.

An dai tsayar da ranar 23 ga watan nan na Maris ne domin sake gudanar da zabukan a cikin wasu mazabu na jahohin da aka ambata.

Babban sakataren jam’iyyar ta APC Lanre Issa-Onilu ya zargi baturen zabe na hukumar zaben kasar Oba Effange da hada baki da jam’iyyar PDP akan zaben gwamna Nyesom wike a jahar Rivers.

A gefe daya, hukumar zabe ta kasar Najeriya ta sanar da janye batun sake maimaita zaben jahar Bauchi, inda ta ce daga  yau Talata za a ci gaba da sanar da sakamakon zabukan karamar hukumar Tafawa Balewa da kuma wasu mazabu na karamar hukumar Ningi.