Hatsarin Jirgin Kasa Ya Ci Rsayukan Mutum 32
Rahotani dake fitowa daga jamhoriyar Dimokaradiyar kwango sun ce kaucewar da wani jirgin kasa ya yi daga kan hanyarsa ya yi sanadiyar mutuwa da jikkatar mutune 123 a kasar
Hukumar gidan talabijin da Radio na kasar Iran ya nakalto hukumomin kasar Congo na cewa hatsarin jirgin kasan, ya auku ne ranar Lahadin da ta gabata a jihar Kasai.
Jami'an 'yan sandar jamhoriyar Dimokaradiyar Congo sun sanar da cewa jirgin kasan da ya yi hatsarin, na dauke da wasu matafiya da aka yi safarar su daga wasu kasashe, sannan kuma mafi yawa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar hatsarin, kananen yara ne.
Rahoton 'yan sandar ya ce daga cikin mutane 91 da suka jikkata, 18 na cikin mawuyacin hali.
A cikin shekarun baya-bayan nan dai ana yawan samu hatsarin jirgin kasa a kasar Dimokaradiyar Congo, inda masana ke danganta lamarin da tsufan jiragen kasar.