Mar 20, 2019 05:31 UTC
  • Harin Bindiga Ya Ci Rayukan Mutum 4 A Kasar Masar

Wani dan bindiga ya buda wuta a jihar Aljiza ta kasar Masar tare da kashe mutum 4 da kuma jikkata wasu 3 na daban

Kamfanin dillancin labaran Irna na nakalto kafafen yada labaran kasar Masar na cewa a jiya Talata, wani dan bindiga ya kai hari garin Awsim na jihar Aljiza, tare da kashe mutum 4 da jikkata wasu 3 na daban.

Jami'an 'yan sandar garin Awsim sun sanar da cewa biyu daga cikin wadanda aka jikkatan, jami'an 'yan sanda ne.

Rahoton ya ce wannan hari na zuwa ne ,bayan wani rikici da ya barke tsakanin wasu kabilun yankin, kuma tuni aka hallaka maharin.

A wani Rahoto da jami'an tsaron 'yan sandar na kasar Masar suka fitar, ya ce rikici da fada tsakanin kabilu da mazauna kauyuka, na salwanta rayukan mutane da dama ko wata shekara a kasar ta Masar.