Afrika Ta Tsakiya: An Cimma Matsaya Kan Kafa Gwamnati
(last modified Thu, 21 Mar 2019 05:54:28 GMT )
Mar 21, 2019 05:54 UTC
  • Afrika Ta Tsakiya: An Cimma Matsaya Kan Kafa Gwamnati

Kungiyar tarayya Afrika ta sanar da cewa, hukumomin Jamhuriya Afrika ta tsakiya da gungun kungiyoyin masu dauke da makamai 14 da suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya sun cimma matsaya kan batun kafa gwamnati.

Bangarorin sun cimma wannan matsaya ce da zata bada damar kafa gwamanti da zata samun wakilcin dukkan bangarorin, a birnin Adis Ababa na kasar Habasha a wannan Laraba, kamar yadda kwamishinan kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar ta (AU), Smaïl Chergui, ya sanar a shaffinsa na Twitter.

A jiya ne dai wasu gungun kungiyoyin masu dauke da makamai 11 daga cikin 14 da suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, suka bukaci fira ministan kasar, Firmin Ngrebada, da ya yi murabus.

Gungun kungiyoyin dai na korafi ne kan rashin samun wakilci a gwamnatin hadin kan kasar, kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma a cen baya a shiga tsakanin kungiyar tarayya Afrika a Adis Ababa ta tanada.