Najeriya: Ana Samun Nasara Wajen Yaki Da Zazzabin Lassa
An sami koma bayan yaduwar zazzabin Lassa A Najeriya A Cikin 2019.
Babban daraktan Asibitin Kwararru na jahar Edo, Prof. Sylvanus Okogbenin ne ya bayyana cewa an sami raguwar masu mutuwa saboda kamuwa da cutar.
Okogbenin ya fadawa kamfanin dillancin labarun Najeriya (NAN) a jiya Laraba cewa; A cikin wannan shekarar ta 2019 an sami raguwar alkaluman masu mutuwa daga cutar da kasa da goma, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Babban daraktan na asibitin Jahar Edo, ya kuma bayyana cewa; an sami wannan gagarumin ci gaban ne saboda aiki tare da aka yi a tsakanin ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayya da hukumar dake dakile yaduwar cutuka da kuma hukumar lafiya ta kasa da kasa.
Okogbenin ya kuma kara da cewa; An kafa cibiya ta nazarin cutar zazzabin Lassa a shekarar 2017, wanda kuma Asibitin kwararru na Edo ya shige gaba wajen taka rawa a wannan fagen.
Ita dai cutar zazzabin Lassa ta samo asali ne daga jahar Borno fiye da shekaru 40 da suka gabata, kuma take da alaka daga bera. Daga lokaci zuwa lokaci akan samu bullar cutar a sassa daban-daban na Najeriya da ma wasu kasashe na yammacin Afirka.