Unicef : Yara 932 Aka Kashe A Hare-haren Sama A Yemen
Wakilin asusun Unicef ne a Yemen ya shaida hakan ga kanfanin dilancin labaren Tasnim na Iran
Asusun kula da yara na MDD wato Unicef ya sanar da cewa yara 932 ne aka kashe a kasar Yemen ta hanyar hare-haren sama da kawacen da Saudiyya ke jagoran ta kasar ya kai a cikin shekara 2015.
kanfanin dilancin labaren Tasnim na kasar Iran, ya ambato wakilin hukumar ta Unicef a kasar ta Yemen Julien Harneis na fadan haka tareda nuna damuwar sa kan halin da kananan yara ke ciki a kasar ta Yemen.
Wannan al'amarin dai a cewar Mr Julien ya shafi illahirin jihohin kasar ta Yemen sakamakon barin wuta da jiragen sama da Saudiyya ke jagoran ta ke ci gaba da kai a wannan kasa.
Wakilin na Unicef ya kara da cewa halin da kasar ke ciki dama tabarbarewar tattalin arzikin ta ya hadasa koma baya matuka wajen isar da kayan agaji da abinci zuwa ga mabukata.