Hukumar Tsaron Amurka Ta Tabbatar Da Kaiwa Kakakin (IS) Hari
Hukumar tsaron Amurka ta gaskata cewa, kawacen kasa da kasa dake yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta ISIS karkashin jagorancin kasar ya kaiwa kakakin kungiyar ta IS Abu Mohammed al-Adnani hari wanda ya hallaka shi a farkon wannan mako.
Cikin wata sanarwar da kakakin hukumar tsaron kasar Amurka Peter Cook ya fitar, an ce, an kaiwa al-Adnani harin ne a Lardin Aleppo na kasar Syria.
Dama kafin hakan kungiyar ta IS ta sanar cewa an kashe daya daga cikin manyan shugabaninta, kuma kakakin kungiyar Abu Mohammed al-Adnani, lokacin da aka kai hari kan motar da yake ciki yayin da take tafiya a yankin da ake kira al-Bab a arewa maso gabashin Aleppo.
Rahotanni suna nuni da cewa al-Adnani ya gamu da ajalinsa ne sakamkon harin da Amurka ta kai da jiragen yaki, amma jami'an tsaron Amurka suna cewa sun auna harin ne kan wani babban jami'in kungiyar ISIS.