An Kashe 'Yan Ta'adda 12 A yankin Sinaa Na Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i10759-an_kashe_'yan_ta'adda_12_a_yankin_sinaa_na_kasar_masar
Jaridar, Yau Sabi'i ta kasar Masar, ta ambato majiyar tsaro na cewa an kashe 'yan ta'adda 12 A Yankin Sinaa.
(last modified 2018-08-22T06:58:54+00:00 )
Sep 08, 2016 02:09 UTC
  • An Kashe 'Yan Ta'adda 12 A yankin Sinaa Na Kasar Masar

Jaridar, Yau Sabi'i ta kasar Masar, ta ambato majiyar tsaro na cewa an kashe 'yan ta'adda 12 A Yankin Sinaa.

Jaridar, Yau Sabi'i ta kasar Masar, ta ambato majiyar tsaro na cewa an kashe 'yan ta'adda 12 A Yankin Sinaa.

Majiyar ta ci gaba da cewa; Sojojin kasar sun kai farmaki ne sansanonin 'yan ta'addar da ke yankunan ( Sheikh Zuwaid) da ( Rafah) da su ke a arewacin tsibirin Sinaa da kuma gabacin   ( al-Arish). Bugu da kari, sojojin sun kona babura shida da 'yan ta'addar su ke amfani da su, da kuma lalata wasu bama-bamai guda uku.

Kungiyoyin 'yan ta'adda sun maida yankin Sinaa ya zama babbar cibiyar da su ke amfani da ita wajen kai hare-hare a cikin kasar ta Masar.

Kungiyar ( Ansaru Baitu Muqaddas) ce mafi hatsari a tsakanin kungiyoin 'yan ta'addar da ake da su a kasar ta Masar.