Bukatar Hizbullah Kan Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kasar Lebanon
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i11293-bukatar_hizbullah_kan_gudanar_da_zaben_shugaban_kasa_a_kasar_lebanon
Ministoci, Jami'an gwamnati da kuma wakilan majalisar dokokin kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon sun yi kira da a gaggauta zaben shugaban kasar ta Lebanon.
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
Sep 20, 2016 00:31 UTC
  • Bukatar Hizbullah Kan Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kasar Lebanon

Ministoci, Jami'an gwamnati da kuma wakilan majalisar dokokin kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon sun yi kira da a gaggauta zaben shugaban kasar ta Lebanon.

Mataimakin babban sakataren kungiyar Sheikh Na'eem Kasim, ya yi karin bayani dangane da wannan bukatar, inda ya bayyana cewa, hanyoyin zaben shugaban kasa a kasar Lebanon a fili suke, kuma dukkanin hanyoyi zasu kai ga zaben Michel Awun ne. Sheikh Na'eem Kasin ya kara da cewa manya manyan kasashen Laranwa masu fada a ji, ko Majalisar dinkin duniya ko kungiyar kasashen Larabawa basu isa su sauya wannan natijar ba.

Mataimakin babban sakataren na Hizbullah ya kara da cewa kara jinkirta zaben Michel Awun a kan kujerar shugaban kasar Lebanon ba abinda zai jawo sai kara cutar da mutanen kasar ta Lebanon ne, don akwai ayyuka da dama wanda shugaban kasa ne kawai zai iya aiwatar da su.

A halin yanzu dai rashin zaben shugaban kasar ta Lebanon ya kai ga a dole aka tsawaita wa'adin zaben wakilan majalisar dokokin kasar, wanda yakamata a gudanar a karshen shekara ta 2014 har zuwa shekara 2017 mai zuwa. Har'ila yau ya zuwa yanzu shekaru 2 da rabi keanen babu wanda ya hau kan kujerar shugaban kasar Lebanon. Hakan kuma wani hatsari ne babban, musamman a bangaren barazanar fadawa cikin rudu da rashin bin doka a kasar.

Wa'adin Mulkin tsohon shugaban kasar Lebanon na karshe wato Michel Sulaiman ya kawo karshe ne a ranar 24 ga watan Mayun shekara 2014, kuma yanzun shekara 2.5 ke nan babu wanda ya hau kan wannan kujerar. 

Babban dalilin da yasa aka kasa zaben shugaban kasa a kasar ta Lebanon dai shine dagewar da gamayyar jam'iyyun siyasa wacce aka fi saninta da "14 ga watan Maris" na cewa sai dan takararsu Samir Jaajaa ne za'a zaba kan kujerar, kuma shi ne kadai suke ganin zai bi ra'ayin kasashen yamma da kawayensu na kasashen Larabawa a harkokin gudanar da kasar. Sai dai a fili yake Samir Jaajaa bai cancanci zama shugaban kasar Lebanon ba, don irin laifuffukan da ya aikata a baya, wadanda suka hada da hannu da yake da shi wajen kisan tsohon Priministan kasar Rasheed Karami a shekara 1987 wanda ya kai ga aka yanke masa hukuncin kisa har sau ukku a gaban wata kotu a kasar, amma aka dawo da hukuncin zuwa daurin rai da rai, shi dimma bayan ya shiga kaso na wani lokaci an sake shi. 

Amma Michel Awun shugaban jam'iyyar "the National Free Movement" kuma shugaban gungun yan majalisar masu son kawo gyara a majalisar dokokin kasar ya cika dukkan sharudda na zama shugaban kasa. 

Tsaron shugabancin siyasa a kasar Lebanon dai shi ne shugaban kasa dole ne ya fito daga bangaren kiristoci daga mazhabar Maronait, sannan Priminista ya zama musulmi dan mazhabar sunna, sannan shugaban majalisar dokokin kasar ya fitom daga musulmi mabiyin mazhabar shia. Banda haka Michel Awun yana da karbuwa a cikin mutanen kasar ta yadda, da za'a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar kai tsaye da mutane zasu zabe shi. 

Don haka ne kungiyar hizbullah a kiraye kirayenta na karshe karshen nan ta bukaci a gaggauta zaben shugaban kasa don kada rashin hakan ya jefa kasar cikin mummunan hali, fiye da wanda take ciki a halin yanzu. Kuma tayi kira ga gamayyar jam'iyyun siyasa ta 14 ga watan Maris su yi hattara don kada su jefa kasar cikin rikici.