Yemen : Jiragen Saman Saudiyya Sun kashe Mutane Sama da 30
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i1153-yemen_jiragen_saman_saudiyya_sun_kashe_mutane_sama_da_30
Wuraren da hare-haren suka shafa sun hada da lardinan al-Matmah da al-Khared dake yankin al-Jow.
(last modified 2018-08-22T06:57:51+00:00 )
Feb 23, 2016 05:04 UTC
  • Yemen : Jiragen Saman Saudiyya Sun kashe Mutane Sama da 30

Wuraren da hare-haren suka shafa sun hada da lardinan al-Matmah da al-Khared dake yankin al-Jow.

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa sama da mutane 30 ne suka rasa rayukan su sakamakon farmakin da jiragen kasar Saudiyyar ke ci gaba da kaiwa a kasar.

Galibin wadanda hare-haren suka rusa dasu fararen hula ne da suka hada da mata da yara kanana a cewar rahotannin.

Bayanai sun nuna cewa an kai hare-hare har sau biyar wanda suka hada da kan motocin jama'a da kuma motocin fasinja.

Wuraren da hare-haren suka shafa sun hada da lardinan al-Matmah da al-Khared dake yankin al-Jow.