Sojojin Yamen Sun Kashe Wani Kwamandan Alqaeda.
Sep 26, 2016 15:50 UTC
An Kashe Dan Alqaeda A Kasar Yamen
Sojojin Yamen sun sanar da kashe wani kwamandan kunkiyar alqa'eda a gundumar Abyan.
Majiyar sojan na Yamen ta kara da cewa; Sojojin Sun kutsa gidan da Abdullah Hubaibat ya ke a garin Loder da ke gundumar Abyan inda su ka kashe shi.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ce; Sojojin na Yamen sun kuma jikkata wasu 'yan ta'addar biyu, sai dai daya daga cikin sojojin ya rasa ransa.
Kasar ta Yamen dai tana fuskantar yakin da Saudiyya ta shelanta a kanta, fiye da shekara da daya.