Tsohon Shugaban Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ya Mutu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i11680-tsohon_shugaban_haramtacciyar_kasar_isra'ila_ya_mutu
Asibitin ( Sheba Medical Center ) da ke Tel Avivi ya bada labarin mutuwar Shimon Peres sa'oi kadan da su ka gabata.
(last modified 2018-08-22T06:59:00+00:00 )
Sep 28, 2016 03:56 UTC
  • Tsohon Shugaban Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ya Mutu

Asibitin ( Sheba Medical Center ) da ke Tel Avivi ya bada labarin mutuwar Shimon Peres sa'oi kadan da su ka gabata.

Majiyar ta ce; Shimon Peres ya mutu ne da misalin karfe 3;40 na daren da ya gabata bayan bugawar kwakwalwarsa.

Tun a jiya talata ne dai dangin Peres suka sanar da cewa yana cikin matsanancin yanayi.

Makwanni biyu da su ka gabata ne dai aka kwantar da Peres dan shekaru 93 a asibiti.

A lokacin da ya ke a raye, Peres, ya tafka laifukan yaki da kuma cin zarafin bil'adama. Daga cikinsu akwai murkushe yunkurin al'ummar Palasdinu da maida dubban palasdinawa zama 'yan gudun hijira da kisan kiyashi a Qana.