Sojojin Syria Sun Shiga Tsakiyar Birnin Aleppo
Sep 28, 2016 03:57 UTC
Sojojin Syria, Sun Kwace Iko Da Tsakiyar Birnin Aleppo daga hannun, 'yan ta'adda
Tashar Telbijin din gwamnatin Syria ta bada labarin cewa; Sojojin Kasar, sun shimfida ikonsu a tsakiyar birnin Aleppo bayan da su ka kori 'yan tadda daga cikinsa.
Majiyar sojan Syrian ta kara da cewa; Yankin Fara-farah, da ke kusa da ganuwar Halab mai tarihi, ya shiga karkashin ikon sojojin kasar, kuma ana ci gaba da fafatawa domin kwace garin baki daya daga 'yan ta'adda.
A jiya talata ne dai sojojin Syria su ka kai hari ta kusuruwowi hudu zuwa cikin garin ta kasa, yayin da jiragen yaki su ka rika aman wuta akan sansanonin 'yan ta'adda.