Ansarullah Ta Yamen Ya Ja Kunnen Amurka
Oct 14, 2016 02:15 UTC
Yeman Ta Gargadi Amurka Akan ci gaba da kai hari
Kungiyar Ansarullah ta kasar Yeman ta ja kunnen Amurka akan ci gaba da kai wa kasar hari.
Kamfanin Dillancin labarun Reuters, ya ambato majiyar Ansarullah ta Yeman a jiya alhamis na maida martani akan harba makamai masu linzami da Amurkan ta yi a kasar ta Yemen sun ja kunnenta da kada ta sake maimaita hakan.
Bugu da kari, kungiyar ta kore cewa ita ce ta harba makami mai linzami akan jirgin ruwan yakin Amurkan.
Harin na Amurka ya lalata cibiyoyin soja ta hanyar harba makamai masu linzami daga jirgin yaki.
Shima kakakin sojan kasar ta Yeman Sharaf Luqman, ya yi tir da kai harin.