Shirye-shiryen Kafa Sabuwar Gwamnati A Kasar Lebanon
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13342-shirye_shiryen_kafa_sabuwar_gwamnati_a_kasar_lebanon
Sabon Pira Ministan Kasar Lebanon Ya Sanar da shirin kafa gwamnati
(last modified 2018-08-22T06:59:11+00:00 )
Nov 03, 2016 14:30 UTC
  • Shirye-shiryen Kafa Sabuwar Gwamnati A Kasar Lebanon

Sabon Pira Ministan Kasar Lebanon Ya Sanar da shirin kafa gwamnati

Kamfanin Dillancin Labarun ' Iran' ya ambato sabon pira ministan kasar ta Lebanon, Sa'ad Hariry, yana cewa; An fara tattaunawa da tuntubar juna domin kafa sabuwar gwamnati wacce ba ta bangaranci ba.

Sa'ad al-Hariry wanda ya ke magana da manema labaru a birnin Beirut cewa; Daga cikin manufofin da su ke a gabansa, da akwai kawo karshen matsalar tattalin arzikin kasar da kuma rashin tsaro da kasar ta fuskanta a cikin shekaru biyu da rabi.

Sabon Pira ministan kasar ta Lebanon  ya jaddada cewa zai iya kokarinsa domin kare kasar daga ayyukan ta'addanci da kuma warware matsalar 'yan gudun hijirar kasar Syria.

A yau alhamis ne dai shugaban kasar ta Lebanon Micheal Aun, ya ayyana Sa'ad al-Hariry a matsayin sabon Pira minista tare da bashi umarnin kafa sabuwar gwamnati.