An Sanar Da Tsagaita Wuta Na Sa'o'i 48 A Yemen
Kawacen da Saudiyya ke jagoranci a Yemen ya sanar da shirin tsagaita wuta na sa'o'i 48 da zai fara aiki da misalin karfe 12 na rana wato karfe 9 ogogon GMT a yau Asabar.
Wata sanarwa da kawacen ya fitar ta ce za'a ma iya sabunta tsagaita wutar idan 'yan Houtsis suka amunce da shirin isar da kayan agaji a wuraren da suke rike da kamar Taez, dake kudu maso yammacin kasar ta Yemen.
Sanar da tsagaita wutar dai ya biyo bayan wata wasika da shugaban kasar ta Yemen mai murabus, Abd Rabbo Mansour Hadi dake gudun hijira a Saudiyya ya aikewa da Sarki Salman.
Sanarwar ta kara da cewa matakin tsagaitar wutar na karfafawa matakin MDD ne da kasashen duniya na samar da zamen lafiya da kuma isar da kayan agaji a kasar Yemen.
Saidai sanarwar ta ce kawacen zai iya kai farmaki a duk lokacin wata barazana ta taso daga 'yan Houtsis ko kuma gungun mayakan dake goyan bayan tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh.
Har kawo lokacin fasara wannan labarin babu wani martani daga bangaren 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsis din a kasar ta Yemen, koda yake a kwana nan sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya sanar da wani shirin tsagaita wuta da zai fara aiki ranar Alhamis wanda 'yan Houtsis din suka amunce da shi.