Siriya ta aikewa MDD wasika kan harin 'yan ta'adda
Ma'aikatar harakokin wajen Siriya ta aikewa MDD da kwamitin tsaro na MDD wasiku kan harin da 'yan ta'adda suka kai kan makarantu Piramire na arewacin birnin Halap wanda ya yi sanadiyar 'yan makarantar Piramire 10.
Kamfanin dillancin Labaran Pars ya nakalto Ma'aikatar harakokin wajen Siriya a jiya Lahadi na cewa wadannan wasiku biyu sun tabbatar wa Duniya cewa ci gaban ta'addanci da kungiyoyin 'yan ta'adda ke yi a kasar, na nuni da cewa goyon bayan 'yan ta'adda ya zamanto siyasar kasa da kasa, kuma maimakon Kwamitin tsaron MDD ya yi alawadai da ta'addanci sai ma ya zamanto yana kokarin kare 'yan ta'addar.
Kasar ta Siriya ta bayyana kyakkyawan fatan ta ga wadanda suke goyon bayan 'yan ta'addar da suke kai hare-hare kan makarantu da asibitoci da su dakatar da taimakon kudi da makamai da suke ba su.
A safiyar jiya Lahadi ne 'yan ta'addar Siriyan suka halba makamai igwai a cikin wasu kananen makarantu biyu harin da ya yi sanadiyar mutuwar yara 'yan Piramire 10.