An kashe Sojin Labanon a arewacin kasar.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i14842-an_kashe_sojin_labanon_a_arewacin_kasar.
Dakarun tsaron Labanon Sun sanar da kashe Sojin su guda a arewacin kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:21+00:00 )
Dec 05, 2016 07:49 UTC
  • An kashe Sojin Labanon a arewacin kasar.

Dakarun tsaron Labanon Sun sanar da kashe Sojin su guda a arewacin kasar

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Dakarun tsaron Labanon a wannan Litinin na cewa harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan cibiyar tsaro ta arewacin kasar ya yi sanadiyar mutuwar Sojin kasar guda da kuma jikkatar wani guda na daban.

A bangare guda kuma wani rahoto  wasu 'yan bindiga sun kai hari kan mai tsaron Khalid Asha'ib babban kwamandan tsaron yankin Palastinu a sansanin Ainul-khalwa dake garin Saida na kasar Labnon, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa, sannan daya daga cikin jigo da jam'iyar Fathu Palastin ya jikkata.