Palasdinu: Harin Sojojin Mamayar 'Yan Sahayoniya A Ramallah.
Dec 07, 2016 12:01 UTC
Sojojin Yahudawa Sun Kame Bapalasdine Guda
Samarin Palasdinawa sun yi taho mu gama da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila a garin Ramallah da ke yammacin kogin Jordan.
Kamfanin Dillancin labarun Palasdinu na "Ma'an" ya nakalto cewa; matasan Palasdinawa sun yi taho mu gama da sojojin yahudawa a cikin birnin Ramallah. Matasan na Palasdinawa dai suna dauke da duwatsu yayin da sojojin na yan sahayoniya su ke rike da manyan makamai.
Tun makwanni uku da su ka gabata ne dai sojojin na yahudawa su ka rufe hanyoyi biyu na shiga kauyen "Deir Nizam".
Palasdinawan na Ramallah dai suna goyon bayan 'yan'uwan nasu ne da sojojin na Sahayoniya su ka killace.
Tags