Harin Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Akan Palasdinawa
Jan 03, 2017 08:46 UTC
Da Safiyar yau talata sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila su ka kai harin a yankuna daban-daban na yammacin kogin Jordan.
Garuruwan da sojojin su ka kai hari sun hada da Nabulus da Bethlaham da Ramalla da Qalqiliyah da Jenin, inda su ka lalata gidaje da dama.
Sojojin na haramtacciyar Isra'ila sun saba kai hare-hare a cikin garuruwan Palasdinawa tare da kame su.
Hukumar Palasdinawa mai kula da fursunonin palasdinawa ta sanar da cewa; Daga farkon boren Intifadar Qudus wacce ta fara a watan oktoba a 2015 zuwa 28 ga watan Decemba 2016, adadin palasdinawan da 'yan sahayoniyar su ka kame, sun kai dubu 9 da 920.
Bugu da kari adadin palasdinawan da su ka yi shahada a wannan tsakanin, sun kai 271.