Netanyahu, Ya Soki Taron Neman Sasanta Isra'ila Da Palestinu
Firaministan yahudawan mamaya na Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya soki taron da Faransa zata jagoranta na farfado da tattaunawar neman sulhu tsakanin Israil'ar da Palestinu.
Netanyahu, ya bayyana yau Alhamis cewa Isra'ila ba tada wata alaka da wannan taron wanda ya ce na kara ruruta wutar kyammar Isra'ila.
A ranar lahadi mai zuwa ce aka shirya gudanar da taron a Paris babban birnin Faransa da nufin lalubo hanyoyin farfado da tattaunawar yin sulhu tsakanin yahudawan mamaya na Isra'ila da kuma al'ummar Palestinu,
Taron dai zai hada wakilan kasashen duniya da kungiyoyi domin kawo karshen rashin fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.
Mahukuntan Palestinu dai sun karbi gayatar taron inda ita kuwa Isra'ilar tayi fatali da gayatar ta Faransa.
An tsara dai a karshen taron na Paris shugaba Farancois Hollande zai gana da shugaban Palastinawa Mahmoud Abass.