Kashi 55% na Al'ummar Yemen na fuskantar matsalar karamcin Abinci.
Kungiyar Samar da abinci ta Duniya Fao ta sanar da cewa fiye da Yamaniwa million 7 ne dake a matsayin kashi 55% na 'yan kasar ke fuskantar fuskantar karamcin abinci.
A wani Rahoton da ta fitar kungiyar samar da Abinci da Noma ta Duniya wato FAO ta ce kimanin Mutane million 7 da 600 ne daga cikin 'yan kasar yemen million 14 ke cikin mawuyacin hali na karamcin abinci.
Rahoton ya ce sama da jihohi 10 ne na kasar ke cikin mayuwacin hali na matsalar karamcin abinci sanadiyar rikicin kasar da ya tunkari shekara daya ana yinsa.
A wata sanarwa da Ma'aikatar masana'antu gami da kasuncin kasar yemen ta sanar, cikin wannan shekara ta 2016 kasar na bukatar Alkama kimanin tom million uku da dubu 827.
har ila yau rahoton ya ce sama da Mutane million biyu da rabi ne suka rasa aiyukan yi sanadiyar rufe masana'antu da hare-haren wuce gona da irin da kawancen saudiya ke kaiwa kan Al'ummar kasar ya janyo.
A bangare guda farshin Man fetur ya yi tashin korbor zabi tun bayan da kawancen saudiya ya fara kai hare-hare cikin kasar inda ya karu da kashi 159%.
Tun daga ranar 26 ga watan Maris din shekarar da ta gabata ce kasar Saudiya tare da wasu kasashen Larabawa bisa amincewar kasashen yamma musaman ma kasar Amurka suka fara kai hare-haren wuce gona da iri a yankuna daban daban na kasar Yemen,lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar duban fararen hula tare da rusa kasar.