Daliban Wata Jami'a A Kasar Ireland Sun Hana Jakadan Isara'ila Jawabi
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i17904-daliban_wata_jami'a_a_kasar_ireland_sun_hana_jakadan_isara'ila_jawabi
Daliban wata jami'a a kasar Ireland sun hana jakadan HKI jawabi a wata Jami'a a birnin Dublin babban birnin kasar a yau Talata
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Feb 21, 2017 14:24 UTC
  • Daliban Wata Jami'a A Kasar Ireland Sun Hana Jakadan Isara'ila Jawabi

Daliban wata jami'a a kasar Ireland sun hana jakadan HKI jawabi a wata Jami'a a birnin Dublin babban birnin kasar a yau Talata

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ce daliban jami'an trinity collage a cikin birnin Dublin sun taru a wasu wurare a cikin jami'ar suna ta rare shee'arai masu nuna cewa suna goyon bayan al-ummar Palasdinu suna kuma yin Alawadai da HKI Isara'ila.

Labarin ya kara da cewa dama an shiryacewa jakadan HKI a kasar ta Ireland  Mr  Ze’ev Boker zai yi jawabi a jami'ar, amma abinda ya faru a wurin da zai yi jawabin a cikin jami'ar ya tilastawa hukumomin jami'ar dage jawabin. 

Daliban wadanda yawansu ya kai 40 wadanda kuma suke kiran kansa Justice for Palatine, wato masu goyon bayan adalaci ga Palasdinawa sun daga tutar Palasdinawa da kuma rubuce rubuce wadanda suke nuna goyon baya ga al-ummar Palasdinu wadanda yahudawan HKI suke gallazawa shekaru aro aro.