Jordan : An Zartas Da Hukuncin Rataya Kan Mutane 15
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18220-jordan_an_zartas_da_hukuncin_rataya_kan_mutane_15
Masarautar Jordan ta sanar da rataye wasu 'yan ta'adda da kuma masu muggan laifuka 15.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 04, 2017 07:11 UTC
  • Jordan : An Zartas Da Hukuncin Rataya Kan Mutane 15

Masarautar Jordan ta sanar da rataye wasu 'yan ta'adda da kuma masu muggan laifuka 15.

Da yake tabbatar da hakan kakakin gwamnatin kasar, Mahmoud al-Momani, ya ce an rataye mutanen ne a gidan yarin Suaga, dake kudancin birnin Amman.

Goma daga mutanen dai ana zarginsu da alaka da wata kungiyar 'yan ta'adda data kai hare hare a wurare da dama na kasar ciki harda kan cibiyar leken asiri da kuma kan jami'an tsaro da kuma kan offishin jadancin kasar a Bagadaza cikin  2003.

Sauren mutanen kuma ana zarginsu da aikata muggan laifuka ciki har da fyade.