An kame Matasan Palastinawa 4 a Ramullah
Jami'an tsaron Haramcecciyar kasar Isra'ila sun yi awan gaba da wasu Matasan Palastinawa 4 a mashigar Aufar ta yammacin garin Ramullah dake yankin Tekun jodan.
Rahotanni dake fitowa daga yankin Palastinu sun tabbatar da kame Matasan yankin 4 a jiya Talata bayan da jami'an tsaron Haramcecciyar kasar Isra'ila suka halbi biyu daga cikin su a mashigar Aufar ta yammacin garin Ramullah.rahoton ya tabbatar da cewa matasan biyu an dauke su a sume sanadiyar harbin su da hayaki mai sanya hawaye.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da Daliban Jami'ar Pirzinte suke gudanar da zanga-zangar Lumana domin nuna bacin ran su kan bindigewar da Jami'an tsaron HKI suka yiwa Shahid Basil A'araj ranar Litinin da ta gabata, a yayin wannan zanga-zanga Jami'an tsaron Sahawuna sun farwa Daliban, lamarin da ya sanya da dama daga cikin su suka suma sandiyar harbinsu da hayaki mai sanya hawaye.
A bangare guda, Jami'an tsaron HKI sun yi awan gada da 'yan Majalisu guda biyu na kungiyar gwagwarmayar nan ta Hamas ranar Litinin da ta gabata a Baitu-Laham, cikin su har da daya daga cikin Komondojin kungiyar.
Bisa alkalumar da kungiyar kare hakin bil-adama ta Palastinu Addamir ta fitar akwai Palastinawa kimanin dubu 7 dake tsare a gidan kurkukun Haramcecciyar kasar Isra'ila.