Martanin MDD kan tsananin take hakin addini na mahukuntan HKI
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18450-martanin_mdd_kan_tsananin_take_hakin_addini_na_mahukuntan_hki
Mataimakin kakakin babban saktaren MDD ya bukaci magabatan HKI da su kiyaye hakokin Addini na Al'ummar yankin Palastinu.
(last modified 2018-08-22T06:59:48+00:00 )
Mar 12, 2017 02:36 UTC
  • Martanin MDD kan tsananin take hakin addini na mahukuntan HKI

Mataimakin kakakin babban saktaren MDD ya bukaci magabatan HKI da su kiyaye hakokin Addini na Al'ummar yankin Palastinu.

A yayin da yake mayar da martani kan sabuwar dokar hana wani bangare na kiran sallah a birnin Qudu,mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq ya bayyana wa manema Labarai a jiya Assabar cewa ya zama dole ga mahukuntar Haramcecciyar kasar Isra'ila su mutunta hakokin Addini na Al'ummar Palastinu.

A ranar Larabar da ta gabata ce Majalisar dokokin haramcecciyar kasar Isra'ila ta amince da wata doka wacce ta haramta kiran sallah da Lasifika daga karfe 11 na dare zuwa 7 na safe a masallatan dake cikin birnin Qudus, wannan matsaya ta MDD kan ci gaba ta take hakkokkin Al'ummar yankin Palastinu da magabatan Haramcecciyar kasar Isra'ila ke yi na zuwa ne bayan kiran da tsohon saktare janar na Majalisar Banki Moon ya yi, inda ya yi alawadai da cin zarafin wurare masu tsarki da kuma take hakkokin Addinin da ake yiwa Al'ummar Palastinu, tare da neman a kawo karshen wannan lamari. 

Yadda mahukuntan Haramcecciyar kasar Isra'ilan ke gudanar da mumunar mu'amala  da Al'ummar Palastinawa shi ke nuna cewa ba sa sauraren dukkanin kiraye-kirayen da kungiyoyin kasa da kasa ke yi, a gurbataccen tunanin su, rushe masallatai da kuma cin zarafin wuraren ibada,gami da kayyade lokaci gami da wurin ibada ga Al'ummar Palastinu na iya hana Palastinawan ci gaba da gwagwarmaya da kuma shagaltar su a kan manufofin su na neman 'yantar da kasar su daga mamaya, wannan sabuwar doka ta kayyade lokacin kiran Sallah a birnin Qudus, ya kara janyo fishin Palastinawa da Al'ummar musulmi a Duniya.

Duk wani abu da a tunanin su  zai dakatar da gwagwarmayar neman 'yanci na Al'ummar Palastinu shi ne mahukantar HKI ke yi, to amma abinda ke wakana a yankin na nuni da cewa wannan mataki babu wani cikas da zai kawo na ci gaba da gwagwarmayar ta Palastinawa,hasali ma dokar na kara bayyana hakikanin manufar Gwamnatin HKI tare kuma da janyo ma ta karin gyama da bakin jini a Duniya, musaman ma a kasashen musulmi da kuma kasashe masu 'yanci na Duniya.

Palastinawa dai sun nuna cewa ba za taba kasa a gwiwa ba wajen kare wurare masu zarki na Al'ummar musulmi ba, kuma tsananta nuna adawa da Palastinawan ke yi a cikin watanin baya bayan nan ga sabin matakan mahukutan HKI na a matsayin fara sabuwar Intifadar kare masallacin Qudus, ko kuma Intifada ta Uku.abinda ke tabbatar da hakan kuwa shi ne yadda Piraministan na HKI ke ci gaba da daukan matakan danne hakkokin Addini a Haramcecciyar kasar Isra'ilan, mahangar Shugaban kasar Amurka Donal Trump na kiyayya da addinin musulinci ya janyo cece kuce a tsakanin Al'ummar musulmi na Duniya, kuma hakan na a matsayin wata rikar kariya na bakar siyasar mahukuntan HKI ga Al'ummar musulmi,

Manarzan yau da kulun na ganin cewa Siyasar Sabon Shugaban Kasar ta Amurka Donal Trump da Piraministan Haramcecciyar kasar Isra'ilan daya ce a fagen cin zarafi da kuma tare hakkokin Addini, musaman ma wajen nuna gyama da yakar Addinin Islama.