Zanga-Zangar Al'ummar Palasdinu Ta Yin Allah Wadai Da Hukumar Palasdinu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18506-zanga_zangar_al'ummar_palasdinu_ta_yin_allah_wadai_da_hukumar_palasdinu
Al'ummar Palasdinu da ke yankin gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa dangane da hada kai da ta yi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a fuskar tsaro.
(last modified 2018-08-22T06:59:49+00:00 )
Mar 14, 2017 08:47 UTC
  • Zanga-Zangar Al'ummar Palasdinu Ta Yin Allah Wadai Da Hukumar Palasdinu

Al'ummar Palasdinu da ke yankin gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa dangane da hada kai da ta yi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a fuskar tsaro.

Al'ummar Palasdinu da suke rayuwa a yankunan gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da matakin da hukumar cin gashin kan Palasdinawa ta dauka na hada kai da gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya a fagen tsaro da nufin murkushe gwagwarmayar Palasdinawa.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa: Hukumar Palasdinawa tana hada kai da mahukunatan haramtacciyar kasar Isra'ila ne wajen kame 'yan gwagwarmayar Palasdinawa da nufin kawo karshen yunkurin kwato yancin Palasdinawa.