Isra'ila ta fara Atisayin Soja
Dakarun tsaron Haramcecciyar Kasar Isra'ila sun fara atisayin Soja a kudancin kasar
Tashar Telbijin din Al'alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa a wannanTalata Dakarun tsaron Haramcecciyar Kasar Isra'ila sun fara atisayin Soja a kudancin kasar, kuma manufar wannan atisayi gyara zama na Dakarun tsaron kasar tare kuma shirin ko ta kwana kan yadda za su kare kudancin kasar kamar yadda Dakarun HKI suka sanar.
Wannan Atisayi na zuwa ne a yayin da ake takun saka tsakanin magabatan HKI da kuma na Siriya bayan da Jirgin yakin HKI ya kai hari a Siriya, a matsayin mayar da martani, Shugaban Kasar Siriya Bashar Al-Asad ya yi baraznar kai hari a filin jirgin saman Tel-Aviv matukar dai Jiragen Yakin na HKI suka sake kai hari birnin Damuscus da kuma filin saukar jiragen Almazah.
Tun bayan da aka fara rikicin kasar Siriya, Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a yankuna daban daban na kasar musaman ma a tsibirin Golan da nufin goyon bayan 'yan ta'adda masu yaki da Gwamnatin Siriya.