Sojojin Kasar Syria Sun kashe Daruruwan 'Yan Ta'adda A Jiya Juma'a
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18812-sojojin_kasar_syria_sun_kashe_daruruwan_'yan_ta'adda_a_jiya_juma'a
A ci gaba da arangama tsakanin dakarun kasar Syria da kuma 'yan ta'addan takfiriyyah da ke samun dauki daga Amurka gami da Turkiya da kuma wasu gwamnatocin kasashen larabawa,a jiya sojojin Syria sun samu nasarar halaka daruruwa daga cikin 'yan ta'addan.
(last modified 2018-08-22T06:59:51+00:00 )
Mar 25, 2017 02:15 UTC
  • Sojojin Kasar Syria Sun kashe Daruruwan 'Yan Ta'adda A Jiya Juma'a

A ci gaba da arangama tsakanin dakarun kasar Syria da kuma 'yan ta'addan takfiriyyah da ke samun dauki daga Amurka gami da Turkiya da kuma wasu gwamnatocin kasashen larabawa,a jiya sojojin Syria sun samu nasarar halaka daruruwa daga cikin 'yan ta'addan.

Rahotanni daga kasar ta Syria sun ce a jiya Juma'a jiragen yakin sojojin kasar sun yi lugudan wuta a kan wasu sansanonin 'yan ta'addan a yankunan gabashin Aleppo da kuma gundumar Hama.

Bayanin ya ce tun daga ranar Talata ta gabata ce 'yan ta'ada suka fara harba makamai masu roka a kan biranan Damascus da Hama, inda a daren Alhamis suka yi yunkurin kutsa kai a wasu yankuna da ke Joubar a ke kusa da birnin damascus, amma dakarun Syria sun halaka mafi yawa daga cikinsu, tare da kame wasu.

Gwamnatin Syria ta dora alhakin hakan a kasashen Turkiya, Qatar da kuma Saudiyya, da ke kashe makudan kudade domin daukar nauyin dukkanin ayyukan ta'addancia  cikin kasar Syria.