Wani Abin Fashewa Ya Kashe Mutum 4 A Bangaladesh
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18844-wani_abin_fashewa_ya_kashe_mutum_4_a_bangaladesh
Rahotanni daga Bangaladesh na cewa mutane hudu ne suka rasa rayukansu kana wasu 42 na daban suka raunana a jerin fashewar wasu abubuwa a yankin da sojoji suka kai samame a wata mabuyar masu kaifin kishin addini.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 26, 2017 01:14 UTC
  • Wani Abin Fashewa Ya Kashe Mutum 4 A Bangaladesh

Rahotanni daga Bangaladesh na cewa mutane hudu ne suka rasa rayukansu kana wasu 42 na daban suka raunana a jerin fashewar wasu abubuwa a yankin da sojoji suka kai samame a wata mabuyar masu kaifin kishin addini.

Daga cikin wandanda suka rasa rayukansu da akwai jami'in dan sanda kamar yadda kakakin 'yan sanda yankin Sylhet dake arewa maso gabashin kasar ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP.

Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kai harin, koda yake 'yan sanda na kasar na zargin kungiyar Jamayetul Mujahideen Bangladesh (JMB) da kai harin.

Wata majiyar asibiti ta shaida cewa akwai mutane da yewa dake cikin mayuyacin hali.

har kawo yanzu dai hukumomin kasar basu yi karin haske ba akan ko harin kunar bakin wake ne ko kuma A'a.