Dakarun Iraki na ci gaba da samun Nasara a Mausul
Dakarun tsaron kasar Iraki sun sanar da 'yanto madatsar ruwa na yammacin garin Mausul
Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalto Manjo-janar Abdul-Amir Yarullah Kwamnadan dake jagorantar rundunar 'yanto garin Mausul na cewa a marecen yau Lahadi Dakarun tsaron kasar sun samu nasarar 'yanto madatsar ruwa na Badush dake yammacin garin Mausul dake mamayar 'yan ta'addar ISIS.
Kwamandan ya kara da cewa har ila yau Sojoji da dakarun sa kai sun kwato Ma'aikatar Siminti, wadil-Ain, da rajumul hadid dake yankin masana'antun yammacin garin na Mausul.
A halin yanzu Dakarun kasar Irakin sun kwato kashi 60% na garin Mausul din, abin da yanzu dakarun za su fi mayar da hanakali kansa shi tsofin anguwani da 'yan ta'addar ISIS suka yi karkuwa da fararen hula a cikin sa.
A ranar 19 ga watan Favrayu ne Dakarun kasar Irakin suka fara aiyukan tsarkake bangaren yammacin garin Mausul.