Karuwar Ta'addancin Isra'ila A Watan Maris
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19082-karuwar_ta'addancin_isra'ila_a_watan_maris
Ta'addancin mahukuntan haramcecciyar kasar Isra'ila a kan Al'ummar Palastinu ya karu sosai a watan Maris din da ya gabata
(last modified 2018-08-22T06:59:54+00:00 )
Apr 03, 2017 01:37 UTC
  • Karuwar Ta'addancin Isra'ila A Watan Maris

Ta'addancin mahukuntan haramcecciyar kasar Isra'ila a kan Al'ummar Palastinu ya karu sosai a watan Maris din da ya gabata

Cibiyar binciken musamman kan Fursunan Palastinawa ta bayyana cewa, mahukuntan HKI na ci gaba da kame kamen Palastinawa ba tare da wani dalili ba, a cikin watan Maris din da ya gabata Jami'an tsaron HKI sun yi awan gaba da Palastinawa 480 daga cikin su akwai Mata 16 da kuma kananen Yara 75.

Duk da cewa a watan Decembar 2016 da ya gabata, Kwamitin tsaron MDD ya samar da wani kudiri, inda a cikin sa ya yi alawadai kan ci gaba da gine-gine Yahudawa a yankin Palastinawa, amma hakan bai hana mahukuntan HKI ci gaba da kuma tsananta ta'addaci da suka saba a kan Al'ummar Palastinu ba, inda daga cikin Mutane 480 da suka kama a watan Maris din da ya gabata, a kwai wakilan Majalisar samar da doka na kungiyar Hamas da kuma wasu ma'aikatan Gwamnatin Palastinu bayan Mata da kananen Yara, har ila yau Mahukuntan HKI sun yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu fursunan Palastinawa,wanda hakan ya sanda adadin wadanda aka yankewa irin wannan hukunci ya haura zuwa 500.

A halin da ake ciki, ta'addancin mahukuntan HKI bai tsaya ba a kan kame-kame, hukuncin daurin rai da rai gami da gine gine a yankunan Palastinawa ba, a ranar 30 ga watan Maris din da ya gabata da ya kasance ranar kasa ga Al'ummar Palastinu, Majalisar zartarwa ta HKI ta amince da wani kudiri na gina wasu sabin Gidaje a yankunan Palastinu,Walid Ussaf Shugaban Kwamitin kalubalantar gine ginen Yahudawa a yankunan Palastinawa ya bayyana cewa dalilin da ya sanya mahukuntan HKI suka amince da sabin gine gine da gabar tekun Jodan shi ne ci gaba da kokari wajen rarraba yankuna Palastinawa ta yadda gurin su zai cika wajen mamaye kasar Palastinu baki daya.

Magabatan HKI na son nuna cewa babu wani kudiri na kasa da kasa da zai iya hana su cimma gurinsu da kuma ta'addancin da suke aiwatarwa kan Al'ummar Palastinu, har ila yau magabatan HKI na amfani da sabuwar Gwamnatin Amurka ta Donal trump kan damar da ta bata na aiwatar da abinda take so, da kuma yadda aka sanya rikici da yaki ta hanyar samar da 'yan ta'adda a gabas ta tsakiya musaman ma rikicin kasashe Siriya da Iraki wanda hakan zai doke hankulan Duniya game da ta'addancin da ake yi wa Al'ummar Palastinu, kuma wannan wata dama ce da magabatan HKI ke amfani da shi wajen ci gaba da ta'addanci ga Al'ummar Palastinu ta yadda za su dakatar da Intifadar Qudus.

Baya ga Hakan, ta'addancin da magabatan HKI ke ci gaba da yi ya sanya Yahudawan dake zaune a Baitul-Makdis kokawa, Dariruwan Yahudawan sun yi zanga-zanga ta yin alwadai da ta'addancin mahukuntan HKI, inda suka bayyana cewa ci gaba da mamayar da mahukuntan HKI ke yi na yankunan palastinawa ya hana tabbatar da sulhu gami da zaman lafiya a yankin.