Birtaniya Ta yi Burus Da Neman Dakatar Da Sayarwa Saudiyya Makamai
Jaridar Guardian ta Birtaniya ta ce; Pira ministar kasar tana ci gaba da kulla yarjejeniyar sayarwa da kasashen yankun tekun Pasha makamai.
Jaridar Guardian ta Birtaniya ta ce; Pira ministar kasar tana ci gaba da kulla yarjejeniyar sayarwa da kasashen yankun tekun Pasha makamai.
Jaridar bugun yau alhamis, ta ci gaba da cewa; Pira minista theresa may babu wani abu da ya ke gabanta, illa sayar da makamai ga kasar Saudiyya, duk da cewa hakan ya sabawa dokokin cikin gidan kasar.
Rahoton ya kuma kara da cewa; Pira ministar kasar ta Birtaniya, ba ta damu da bala'in da ya ke afkuwa a cikin kasar Yemen ba, abinda ya ke nuni da cewa babu batun jin kai da kare hakkin bil'adama a cikin siyasar wajen kasar Birtaniya.
Kasashen Birtaniya da Amurka da Jamus da Faransa suna cikin kasashen da su ke sayarwa da Saudiyya makamai.
Fiye da mutane dubu 11 ne dai Saudiyyar ta kashe a kasar Yemen, a cikin shekaru biyu na yakin da ta fara akan al'ummar wannan kasa.