Ci Gaba Da Samun Nasarar Dakarun Kasar Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19528-ci_gaba_da_samun_nasarar_dakarun_kasar_yemen
Sojoji da Dakarun sa kai na Kasar Yemen na ci gaba da samun nasara a kan Sojoji mamaya na Saudiya da kawayanta
(last modified 2018-08-22T06:59:58+00:00 )
Apr 17, 2017 13:43 UTC
  • Ci Gaba Da Samun Nasarar Dakarun Kasar Yemen

Sojoji da Dakarun sa kai na Kasar Yemen na ci gaba da samun nasara a kan Sojoji mamaya na Saudiya da kawayanta

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya habarta cewa cikin wani farmaki da Sojoji tare da Dakarun sa kai na kasar Yemen suka kai a wannan Litinin sun samu nasarar dakile ci gaba da mamayar Sojojin hayar Saudi-arabiya da magoya bayanta a yankin Karash dake jihar Lahaj na kudancin kasar, lamarin da ya sanya dakarun mamayar ja da baya.

Har ila yau Sojojin da kuma Dakarun sa kai na kasar Yemen din sun kai hari kan barikin Sojin Assadarain na yankin Maris dake cikin Jihar Dali'i na kudancin kasar tare da hallaka ko jikkata wani adadi mai yawa na dakarun hayar Saudiyan, baya ga haka Dakarun sa kai na Kungiyar Ansarullah sun samu nasarar tarwatsa motocin yaki uku na Sojojin hayar Saudiya a kudu maso yammacin jihar Ta'az.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata Sojojin hayar Saudiya da dama ne suka hallaka sanadiyar hare-haren da Sojoji gami da Dakarun sa kai na kasar Yemen suka kai musu a yankunan Zubab da Almakha dake jihar Ta'az, haka zalika a jihohin Najran, Jizan gami da Asir, Dakarun sa kai na kungiyar Ansarullah  sun hallaka Sojojin haya na Saudiya da dama.