Isra'ila Na Kokarin Kisan Gilla Ga Fursinonin Palastinawa
A ci gaba da take-taken mahukuntar HKI na tsananta azabtar da fursunonin Palastinawa, daya daga cikin magabatan kasar ya bukaci a zartar da hukuncin kisa ga firsinonin da suka shiga yajin cin abinci.
A yayin tuni da ranar fursunonin Palastinawa wato ranar 17 ga watan Avrilu, sama da Fursunonin Palastinawa dake daure a gidajen kaso daban daban na HKI 700 ne suka shiga yajin cin abinci, Yisrael Katz Ministan sadarwa da sufuri na HKI ya bayyana cewa amsar da ya kamata a baiwa masu yajin cin abinci daga cikin fursinonin Palastinawa, zartar da hukunci kisa a kansu kuma akwai bukatar sake tura wannan bukata a gaban Majalisar Dokokin kasar domin samun amincewa.
Baya ga wannan Ministan ya gabatar da shawar kissan killar Palastiwa a maimakon yin awan gaba da su wanda hakan a cewar sa shi zai kawo karshen musayar Fursunoni da magabatan HKI ke yi tare da kungiyoyin gwagwarmaya na Palastinawa.
Wannan Shawara ta Ministan HKI na zartar da hukuncin kisa ga Fursunonin Palastinawa ta sabawa dokar kasa da kasa, da kuma dokokin kare hakin bil-adama gami da yarjejjeniyar Ganeva ta uku da ta hudu da kuma Dokokin Majalisar Dinkin Duniya.
Shuru da kuma halin ko in kula da Duniya ke yi wajen kisan killar da mahukuntar HKI ke yiwa Al'ummar Palastinu, shi ke kara basu damar ci gaba da mumunar siyasar su ta wariya da kuma kisan gilla a kan Palastinawa
Wannan ba shi ba ne karo na farko da magabatan HKI ke son ganin bayan Palastinawa, daga cikin su har da Fursunonin dake tsare da gidan yarin su, so da yawa magabatan HKI sun firta aniyarsu ta siyasa wariya da kuma kawo karshen Al'ummar Palastinu a cikin kasar su da suka mamaye.a cikin 'yan kwanakin da suka gabata tsohon ministan tattalin arzikin HKI kuma Ministan Ilimi a yanzu Naftali Bennett ya bukaci da aka kashe Fursunonin Palastinawa dake cikin gidajen kason HKI.saboda a cewar sa ko da an sake su ,su ne sahun gaba wajen gwagwarmayar neman yancin kasar Palastinu da kuma yakar Isra'ila, domin hakan a ganinsa abinda ya fi dacewa a ciga da yi musu azaba a gidan yari ta yadda za su rasa rayuwarsu.
Irin wannan firici na magabatan HKI na zuwa ne a yayin da Jami'an tsaron Isra'ila ke kara kaimi wajen ganin sun kawo karshen Palastinawa musaman ma fursinonin dake tsare a gidajen kaso daban daban na Isra'ila.
A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, Cibiyar dake kula da fursunonin Palastinawa tare nema musu 'yanci Wato Wa'id ta bayyana cewa ganin cewa Gwamnatin HKI ba ta sanya hannu kan dokokin hana azabtar da Fursinoni ba,hakan ya bata damar take duk wasu hakkoki na kasa da kasa da kuma cibiyoyin kare hakin bil-adama, ci gaba kuma da shuru na Kungiyoyin kasa da kasa ga wannan ta'addanci shi ke sanya magabatan HKI ke kara kaimi wajen azabtar da fursunonin Palastinawa dake tsare a gidajen Yarin HKI ta yadda a halin dake ciki lamarin ya shiga cikin yanayi mai hadarin gaske na kisan gilla.