Sayyid Nasrullah: Isra'ila Ta Yarda Da Kayin Da Ta Sha
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i20284-sayyid_nasrullah_isra'ila_ta_yarda_da_kayin_da_ta_sha
A yayin da yake bayyani kan kudirin magabatan HKI na gina Katangar raba yankin Palastinu da kasar Lebanon Shugaban Kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewa Hakan Shi ke nuna cewa magabatan HKI sun bayyana kasawarsu a fili wajen zartar da kudirin samar da babbar Haramtacciyar kasar Isra'ila.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
May 11, 2017 14:45 UTC
  • Sayyid Nasrullah: Isra'ila Ta Yarda Da Kayin Da Ta Sha

A yayin da yake bayyani kan kudirin magabatan HKI na gina Katangar raba yankin Palastinu da kasar Lebanon Shugaban Kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewa Hakan Shi ke nuna cewa magabatan HKI sun bayyana kasawarsu a fili wajen zartar da kudirin samar da babbar Haramtacciyar kasar Isra'ila.

A yayin da yake gudanar da jawabi albarkacin zagoyowar ranar cikar shekara na shahadar Mustapa Badruddin a marecen wannan Alkhamis da ya gudana a babban dakin taro na Sayyidi Shuhada'a dake gefen kudancin birnin Beirut, Sayyid Hasan Nasrullah Shugaban Kungiyar Hizbullah ya ce a halin da ake ciki, Dan kasar Lebanon na iya tsallaka iyala ya shiga cikin Palastinu har ma ya ci kilomita 10, wannan shi ke nuna cewa dukkanin matakan tsaron da mahukuntanHaramtacciyar kasar Isra'ila ke dauka a wannan yanki ba shi da wani amfani, domin haka ne ma suka dauki kudirin gina katangar da za ta raba kan iyakokin kasashen.

Sayyid Hasan Nasrullah ya tabbatar da cewa gina wannan katanga shi ke nuna cewa nasarar da kasar Lebanon ta samu da kuma kasawar Sahayuna na cimma manufarsu ta samar da babbar Haramtacciyar kasar Isra'ila.

A yayin da yake Ishara kan ziyarar da Shugaban kasar Amurka Donal Trump zai kai kasar Saudiya a kwanaki masu zuwa, Shugaban Kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa a 'yan kwanaki masu zuwa Shugaban kasar Amurka zai ziyarci kasar Saudiya inda zai  gana da magabatan kasar  kuma a cikin wannan ganawa  za mu ga cewa shin za a biya bukatun fursinonin Palastinawa dake yajin cin abinci a gidajen kurkuku na magabatanHaramtacciyar kasar Isra'ila ko kuma A'a, ko da yake mu nada labarin sakamakon Zaman, amma Al'ummar musulmi za ta zura ido domin ganin yadda sakamakon zaman zai kasance.

Yayin da yake ishara kan irin nasarorin da kungiyar Hizbullah ta samu wajen tsarkake kan iyakokin kasar daga 'yan ta'adda, Sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewa bayan samun nasara na fitar da mayakan 'yan ta'adda a yankunan Kalamun da Zabdani da hakan ya tabbatar da tsaro a kan iyakokin gabashin kasar da Siriya, babu wani dalili kuma da zai sanya mayakan Hizbullah su ci gaba da zama a wannan yankuna.