An Cabke Wanda Ya Kashe Mazin Fukaha A Birnin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i20290-an_cabke_wanda_ya_kashe_mazin_fukaha_a_birnin_gaza
Shugaban Kungiyar Hamas ya sanar da cabke wanda ake zarki da kashe Mazen Faqha daya daga cikin komondijin Kungiyar a birnin Gaza.
(last modified 2018-08-22T07:00:05+00:00 )
May 11, 2017 14:47 UTC
  • An Cabke Wanda Ya Kashe Mazin Fukaha A Birnin Gaza

Shugaban Kungiyar Hamas ya sanar da cabke wanda ake zarki da kashe Mazen Faqha daya daga cikin komondijin Kungiyar a birnin Gaza.

Mazen Faqha wanda ya kwashe shekaru da dama a gidan yarin Haramcecciyar kasar Isra'ila an bindige shi ne a ranar 24 ga watan Maris din da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya nakalto Ismael Haniyah Shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas cikin wani taron manema labarai da ya gudanar  wannan Alkhamis a birnin Gaza ya ce mutuman da ya bindige Mazen Faqha ya shiga hanun jami'an tsaron birnin Gaza, kuma shakka babu wannan mutum na zartar da umarnin magabatan Haramcecciyar kasar Isra'ila ne.

Ya zuwa yanzu da dama daga cikin Palastinawan da aka sako daga gidajen yarin Haramcecciyar kasar Isara'ila ne suka yi shahada bayan da Sojojin haya na Gwamnatin HKI suka bindige su daga cikin su har da shi kansa Mazen Faqha.