Hallakar Sojojin Hayar Saudiya A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i20394-hallakar_sojojin_hayar_saudiya_a_yemen
Majiyar tsaron yemen ta sanar da hallaka wani adadi na Sojojin hayar Saudiya a jihohin Jauf da Ta'az.
(last modified 2018-08-22T07:00:06+00:00 )
May 15, 2017 01:56 UTC
  • Hallakar Sojojin Hayar Saudiya A Yemen

Majiyar tsaron yemen ta sanar da hallaka wani adadi na Sojojin hayar Saudiya a jihohin Jauf da Ta'az.

Tashar telbijin din Almasira ta kasar Yemen ta nakalto majiyar tsaron yemen a wannan Litinin na cewa wasu daga cikin sojojin hayar saudiya sun yi kokarin yin kutse a wuraren Sojojin da dakarun sa kai na kasar a yankin Wadiyi Shawak dake jihar Aljauf, saidai sun kamu da tarwatse bama-bamai, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka da kuma jikkatar wani adadi mai yawa daga cikin su.

A jiya lahadi ma Dakarun sa kai na kasar sun kai hari kan dakarun hayar saudiyar a gabashin Almakha dake jihar Ta'az tare da hallaka biyu daga cikin su da tarwatsa wata Motar Soja ta Sojojin hayar saudiyar, har ila yau Dakarun na Yemen sun kai farmaki kan barikin Sojin Salan tare da hallaka wani sojin hayar Saudiya guda.

A bangare guda MDD na kokarin samar da yarjejjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu dake fada da juna a kasar ta yemen daidai lokacin da ake shirye-shiryen watan Azimi mai alfarma.

Tun daga watan Maris na shekarar 2015, magabatan kasar Saudiya suka fara kai farmaki kasar Yemen bisa da'awar mayar da tsohon shugaban kasar da yayi murabus Abdu Rabahu Mansur Hadi, lamarin da ya lashe rayukan Mutane sama da dubu 12.