Qatar Ta Sake Watsi Da Zarge-zargen Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i21722-qatar_ta_sake_watsi_da_zarge_zargen_saudiya
Kasar Qatar ta yi watsi da zarge-zargen goyan bayan ta'addanci da Saudiya da kawayenta keyi mata.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 28, 2017 06:35 UTC
  • Qatar Ta Sake Watsi Da Zarge-zargen Saudiya

Kasar Qatar ta yi watsi da zarge-zargen goyan bayan ta'addanci da Saudiya da kawayenta keyi mata.

Ministan harkokin wajen Qatar, Mohammed ben Abderrahmane Al-Thani, ya ce kasarsa tana da niyyar shiga tattaunawar kawo karshen rikici diflomatsiya da abokan gabanta, muddin dai suka gabatar da kwararen hujjoji akan zargin da suke mata na taimakawa ayyukan ta'addanci.

Kalamen na Mista Al-Thani na zuwa ne bayan ganawarsa da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson a birnin Washigton.

Kafin hakan dai ministan harkokin wajen Saudiya, Adel al-Jubeir ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa babu batun tattaunawa kan bukatun nan 13 da aka gindaya ma Qatar din.