Unicef: An Fuskantar Karancin Kayan Aiki A Cikin Asibitocin Kasar Yemen.
Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce; Killacewar da Kasar Sudiyyar ta yi wa Yemen ne ya hana a shigar da magunguna da kayan aiki cikin kasar.
Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce; Killacewar da Kasar Sudiyyar ta yi wa Yemen ne ya hana a shigar da magunguna da kayan aiki cikin kasar.
Asusun na kananan yara ya ci gaba da cewa; a halin da ake ciki a yanzu suna kokarin jigilar kayan aiki da kuma magunguna domin fuskantar cutar kwalara da ta barke a cikin kasar ta Yemen.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce adadin mutanen kasar ta Yemen da su ka kamu da cutar ta kwalara sun kai 200,000.
Tun a 2015 ne dai Saudiyya ta shelanta yaki akan al'ummar kasar Yemen wanda kawo ya zuwa yanzu ta kashe mutane 12,000, bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.