An Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Rikicin Yemen
-
Yakin Saudiyya Kan Al'ummar Kasar Yemen
Kungiyoyin siyasa a kasar Yemen da kuma wasu gwamnatoci na duniya sun jaddada wajabcin kawo karshen yakin da Saudiyya ta ke yi a kasar Yemen.
Abu Malik Alfaishi mamba a kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa, jam'iyyun siasa da kungiyoyi masu zaman kansu a Yemen ba su da wata matsala da batun dakatar da bude wuta.
Tun kimanin shekara guda ta gabata ce dai kasar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare da manyan makamai kan biranan kasar Yemen, da sunan tana yaki da 'yan kungiyar Ansarullah ko kuma Alhuthi, inda kididdigar majalisar dinkin duniya t ce a cikin watannin da suka gabata Saudiyya ta kashe dubban fararen hula da suka hada da kanan yara da mata, tare da rusa daruruwan makarantu da masallatai da asibitoci da masana'antu da sauransu.