Dakarun Yemen Sun Dakile Harin Sojojin Hayar Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i21790-dakarun_yemen_sun_dakile_harin_sojojin_hayar_saudiya
Dakarun tsaron kasar Yemen sun dakile wani hari da Sojojin hayar Saudiya suka kai jihar Marib tare da hallaka wani adadi mai yawa daga cikin su.
(last modified 2018-08-22T07:00:19+00:00 )
Jun 30, 2017 13:42 UTC
  • Dakarun Yemen Sun Dakile Harin Sojojin Hayar Saudiya

Dakarun tsaron kasar Yemen sun dakile wani hari da Sojojin hayar Saudiya suka kai jihar Marib tare da hallaka wani adadi mai yawa daga cikin su.

Tashar Telbijin din Al-alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto majiyar tsaron kasar Yemen na cewa Dakarun hadin gwiwar kasar sun samu nasarar dakile wani harin mamaya da Sojojin hayar Saudiya suka kai Tsaunin  Alhamra'a na yankin Wadil-Rabi'i da rokoki, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka da kuma jikkatar 40 daga cikin su 

Majiyar ta ce Dakarun tsaron Yemen din tare da Dakarun sa kai sun yi nasarar cabke wasu Sojojin hayar Saudiya masu yawa bayan da suka yi musu kofar raggo.

Tun daga watan Maris din 2015 ne kawancen Saudiya tare da samun goyon bayan kasar Amuka suka fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen tare kuma da killace kasar ta sama, kasa da ruwa bisa da'awar dawo da tsohon Shugaban kasar da yayi murabus Abdu Rabahu Mansur Hadi a kan karagar milki, Harin da ya zuwa yanzu yayi sanadiyar shahadar mutane sama da dubu12 tare da yin sanadiyar jikkatar wasu dubai na daban tare da raba wasu milyoyi da gidajen su.