Qatar Ta Yi Fatali Da Sharuddan Makwabtanta
Kasar Qatar ta yi watsi da sharuddan da Saudiyya da makwabtanta Larabawa suka gindaya mata kafin su sake maido da hulda da ita.
Ministan harkokin wajen kasar Qatar, Mohammed ben Abdurrahman Al-Thani, ya bayyana cewa dama sharuddan da aka gindaya ma kasarsa an yi su ne dama don a yi watsi dasu, saboda sun saba wa 'yancin da cin gashin kan kasar.
A ranar 22 ga watan Jiya ne kasashen Larabawan suka gindaya wa Qatar din shaduddan guda 13 da suka hada da rufe gidan talabijin na Al Jazeera, da rufe wani sansanin sojin Turkiya dake kasar sai kuma rage alakarta da kasar Iran.
A cikin daren Jiya ne dai wa'addin kwanaki 10 da makoftan na Qatar a yankin tekun Pasha da suka hada da Saudiyya, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Masar a daya bangare ya cika.
Qatar ta ce a yau Litini za ta bada amsa a hukumance kan jerin sharuddan a wata wasika da sarki sheikh Tamim ben Hamad Al-Thani ya rubuta wa takwaransa na Kuwait sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah wanda ke shiga tsakani a rikicin diflomatsiya na tsakanin bangarorin.
A wani labari kuma dake fitowa da sanyin safiyar yau, Saudiyya da kawayenta sun karawa Qatar wa'adin sa'o'i 48 a kan wa'addin da suka bata wanda ya kawo karshe a cikin daren jiya.
Kasashen dai na zargin Qatar da taimaka wa ayyukan ta'addanci, batun da Qatar din ta jima tana musuntawa.