"UNICEF" Miliyoyin Kananan Yara Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasar Yamen
Asusun Kula da Kananan Yara da Mata na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya sanar da cewa: Miliyoyin kananan yara suna bukatar tallafin jin kai na gaggawa a kasar Yamen.
Asusun Kula da Kananan Yara da Mata na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya fitar da bayanin cewa: Miliyoyin knanan yara a Yamen suna buktar tallafin gaggawa sakamakon mummunan halin da al'ummar kasar suka shiga na rashin kayayyakin kiwon lafiya, abinci da tsabtaceccen ruwan sha, bayan da jiragen saman yakin masarautar Saudiyya suka ruguza duk wasu cibiyoyin kula da lafiya, rumbun tsimin abinci da ma'aikatun kula da tsabtaccen ruwan sha a kasar.
"UNICEF" ta kara da cewa: Hare-haren wuce gona da irin jiragen masarautar Saudiyya da na kawayenta sun rusa makarantu tun daga matakin firamare har zuwa jami'a lamarin da ya haramta wa al'ummar Yamen samun ilimi musamman kananan yara, baya ga bullar cututtuka a tsakanin al'ummar kasar musamman cutar kwalara lamarin da ya tilasta wa mahukunta sanya dokar ta baci a garuruwan Abyan, Aden, Lahij, Dhale da Sayyan domin samun damar shawo kan ci gaba da yaduwar cututtukan.