Gwamnatin Algeria Ta Hana Wani Malamin Wahhabiyawa Shiga Kasarta
-
Mohammad Arifi -Malamin yan ta'adda
Gwamnatin Kasar Algeria ta hana Mohammad Uraifi wani fitaccen
Gwamnatin Kasar Algeria ta hana Mohammad Uraifi wani fitaccen malamin wahhabiyawa dan kasar Saudia shiga kasarta. Jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ta nakalto ministan harkokin addini na kasar Algeria Mohammad Isa yana fadar haka a yau Laraba ya kuma kara da cewa Mohammad Al-uraifi yana da fikra ta yan ta'adda don haka kasarsa ba zata amince masa shiga kasar.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Mohammad Al-uraifi ne ya bada fatar "Jihadin Aure" ga kungiyoyin yan ta'adda da suke kisan mutane a kasashen Siria da Iraqi. Amma malaman ya musanta hakan.
Mohammad Al-Uraifi ya je kasar Algeria ne don halattan wani taron addini a daya daga cikin biranen kasar.
Kasar Saudia ce a gaba gaba wajen goyon bayan yan ta'adda a mafi yawan kasashen musulmi.