Syria / OSDH : An Raunana ''Omar Tchéchène'' Aman Ba'a Kashe Shi Ba
kungiyar kare hakkin bil Adama ta OSDH a Syria ta bayana cewa an yi wa Omar Tchéchène daya daga cikin kwamandodin 'yan ta'adan (IS) munanen raunuka aman ba'a hallaka shi ba, kamar yadda Amurka ta yi hasashe a wani hari data kai a farkon wannan wata.
kungiyar ta OSDH dake da majiyoyi a sassa daban-daban na kasar ta Syria, ta ce ta samu wannan bayanin daga wasu majiyoyi daga kungiyar ta IS a yankin Raqqa dake arewacin kasar.
A ranar Talata data gabata ne wani babban jam'in Amurka da bai so a ambaci sunan sa ba ya bayana cewa mai yiwa ne Omar din ya hallaka tare da wasu 'yan ta'ada 12 a harin da Amurkar ta kai a ranar hudu ga watan Maris.
A bayanin data fitar kungiyar ta OSDH ta ce Omar din wanda ake kira da ''Tchetchene'' an garzaya dashi asibitin Lardin Hassake dake arewa maso gabashin kasar inda wani likita dan ta'ada dan asalin kasashen turai ya yi masa magani.
Dan ta'adan wanda aka saba gani a hotina da jan ghemu, wanda dan asalin Tchetchene ta Georgiya ne, ya kasance mai matsayin ministan yaki na kungiyar 'yan ta'adan Da'esh, kuma idan ana tuna Amurka ta sanaya ladan $ miliyan biyar ga duk wanda zai taimaka da sahihan bayanai da zasu sa a gano inda ya ke.