Limamin Masallacin Kudus Ya Jaddada Wajabcin Ci gaba Da Gwagwarmaya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i22384-limamin_masallacin_kudus_ya_jaddada_wajabcin_ci_gaba_da_gwagwarmaya
Limamin masallacin Kudus Ikramah Sabry, ya fadi cewa; kafa kofar bincike da 'yan sahayoniya su ka yi a bakin masallacin Kudus keta hurumin masallacin ne.
(last modified 2018-08-22T07:00:25+00:00 )
Jul 19, 2017 06:41 UTC
  • Limamin Masallacin Kudus Ya Jaddada Wajabcin Ci gaba Da Gwagwarmaya

Limamin masallacin Kudus Ikramah Sabry, ya fadi cewa; kafa kofar bincike da 'yan sahayoniya su ka yi a bakin masallacin Kudus keta hurumin masallacin ne.

Limamin masallacin Kudus Akramah Sabry, ya fadi cewa; kafa kofar bincike da 'yan sahayoniya su ka yi a bakin masallacin Kudus keta hurumin masallacin ne.

Sheikh Ikramah wanda jaridar al-ra'ay, ta kasar Kuwaiti ta yi hira da shi ya ci gaba da cewa; Kafa kofofin masu na'urorin bincike a masallacin kudus ba tare da tuntubar hukumar masallacin ba, yana a matsayin keta hurumin masallacin ne.

Sheikh Sabry ya jaddada cewa; daukar matakin kafa kofofin yana da alaka da siyasar cikin gida ta haramtacciyar kasar Isra'ila bayan da ake bincike Netanyaho akan handamar kudade.

A ranar juma'ar da ta gabata ne dai sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila su ka hana masallacin kudus a karon farko a cikin rabin karni.