An Hallaka Sojojin Saudiya Da Dama A Kan Iyakar Kasar Yemen
Sojoji da dakarun sa kai na kasar Yemen sun samu nasarar hallaka sojojin Saudiya da dama a yankin Jizan dake kudancin Saudiya.
Tashar Telbijin din Almasira ta kasar Yemen ta nakalto wata majiyar tsaro a kasan na cewa Sojoji da Dakarun tsaron Yemen sun kai wani gagarumin hari a tsibirin Alkumama na sansanin Sojin Algawuya, inda suka hallaka sojojin saudiya masu yawa da kuma tarwatsa wata mota mai sulke gami da kwasar ganima na makamai masu yawa.
Har ila yau Sojoji da Dakarun sa kai na kasar Yemen sun kai farmaki a barikin Soja Aldafiniya na yankin Jizan tare da hallaka Sojojin Saudiya da dama tare da kone wani runbun tsimi na makamai dake cikin wannan Bariki.
Idan ba a manta ba, tun daga watan Maris 2015, Dakarun kawancen saudiya tare da goyon bayan Amurka gami da wasu kasashen larabawa na yankin suka kaddamar da yakin fice gona da iri a kan al'ummar kasar yemen bisa da'awar medo da tsohon shugaban kasar da yayi murabus Abdu Rabahu Mansur Hadi a kan karagar milki,lamarin da yayi sanadiyar shahadar kimanin Yamaniyawa dubu 40 da kuma illata wasu dubai na daban.